Alhamdulillah Matar jarumin kannywood Adam a zango ta haifasa Masa santaleliyar yarinya

Alhamdulillah Matar Jarumin Shirya Fina finan kannywood Adamu Abdullahi zango Wanda kukafi sani da Adam a zango ta haifa masa ya mace.

Matar Jarumi Adam a zango sophiya chalawa ta haifa masa yarinyar yau alhamis hudu ga watan nuwambar shekarar dubu biyu da ashirin da daya 04/11/2021.

Munasamu wannan sanarwar daga shafin officialkannywood Dake Kan Instagram. Masoyan Jarumi Adam a zango sunshiga murna da Farin ciki ganin yadda abun alkairi yasamu tauraron nasu.

Adam a Zango & Sophiya chalawa

Adam a zango da matarsa sophiya chalawa sunyi aure tsawon shekaru biyu kenan Wanda Matar tasa ta kasance Yar kebbi state ce.

An daura auren Adam a zango da sophiya a garin kebbi state inda aka dauko Amarya aka wuto da ita sabon gidan da Adam a zango ya ginasa acikin garin Kaduna.

Saidai Bayan kawo amaryar mutane sunyi tunanin za’ayi shagulgulan biki kamar yadda sauran jaruman kannywood sukeyi idan zasuyi aure saidai jarumin duk baiyi wannan bidi’ar ba Wanda hakan ya matukar bawa masoyansa mamaki a wannan lokacin.

Saidai jarumin ya zabi Shirya walima acikin gidansa kawai inda aka gayyaci Yan uwa da abokan arziki tareda abokan sana’ar Jarumi Adam a zango kamar yadda kuke gani acikin wannan hoton Adam a zango da amaryar tasa an daukesa ne acikin gidan jarumin.

Adam a zango da matarsa

Jaruman kannywood manya da kanana suntaya Adam a zango murnar samun karuwar ya’ mace inda sukai Mai addu’ar Allah ubangiji ya rayata da Imani.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labaran kannywood Dama wakoki cikin sauki Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button