Sadiq Sani Sadiq, Aisha Najamu Izzar so Da producer Abdul Amart Mai Kwashewa sunje aikin Ummarah

Fitaccun jaruman kannywood Sadiq Sani Sadiq, Aisha Najamu Izzar so tareda babban producer a kannywood Abdul Amart Mai Kwashewa sun isah kasar saudiyya domin aikin Ummarah.

Acikin wasu hotuna da producer Abdul Amart Mai Kwashewa ya wallafa a shafinsa na Instagram angansu acikin masallaci a zaune inda aka hango producer Yana addu’a inda a gefe guda Kuma Jarumi Sadiq Sani Sadiq ne yake jan charbi.

A wani dayan hoton Kuma Wanda fitacciyar jarumar kannywood Aisha Najamu Izzar so ta wallafa a shafinta na Instagram an hango jarumar Tsaye acikin masallaci inda take sanye da hijabi ta dauki hotuna masu kyau.

Aisha Najamu Izzar so

Tafiyar ta hada da Sadiq Sani Sadiq, Aisha Najamu Izzar so Dakuma babban producer inda tundaga Kano Suka taso izuwa kasar ta saudiyya domin sauke farali a ranar larabar uku ga watan nuwambar shekarar dubu biyu da ashirin da daya 03/11/2021.

Kucigaba da bibiyar shafinmu domin Samun labaran kannywood cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button