Tabbas maganar da Adam a zango yayi gaskiyace domin akwai Wanda suke da irin wannan halin

Fitaccen jarumin masana’antar kannywood Adam a zango yayi wata magana Wanda zamuce tanada tasiri adai dai wannan lokacin da goguwar siyasa ta kunno Kai ta shekarar 2023.

Jarumi Adam a zango ya bayyana cewar baikamata ace wasu daga cikin masana’antar kannywood suna gaba da juna domin ra’ayin siyasa kokuma sabida bakwa jam’iya daya da mutum.

Adam a zango ya Kara da cewar Shi Dan Apc ne Kuma zai iya tallata kowani mutum indai har zai taimaki kasarsa Koda kuwa Dan jam’iyar PDP ne.

Saidai tabbas maganar da Adam a zango yayi gaskiya ce domin kuwa akwai jaruman kannywood dayawa Wanda idan ra’ayin siyasarku baizo daya dasu ba zasu daina kulaka kokuma sudinga gaba dakai Wanda hakan bashi bane yake nuna kanada kishin jam’iyarka.

Masana’antar kannywood wata masana’antace Wanda Allah ya albarkaceta da mutane daban daban daga fadin najeriya Dama wajenta, hakan Kuma akwai mabanbanta ra’ayi ma’ana Kowa danasa ra’ayin.

A yayin da goguwar siyasa 2023 take dada kunno Kai yanzune ake samun matsaloli daga masana’antar sakamakon banbanci jam’iya Dakuma banbancin ra’ayi.

Saidai Adam a Zango yayi nuni da cewar duk abinda wani Dan kannywood zaiyi yakamata ace Yana saka sana’arsa a farko domin itace Abu mafi mahimmancin acikin Rayuwar tasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button