Kalli Yadda Nafeesat Abdullahi Ta Chashe awajan Shagalin Bude Kamfanin Jambakinta a garin Kano

Jaruma Nafeesat Abdullahi ta bude Kamfanin yin jambaki a inda aka hada wani babban taro domin Yan uwa da abokan arziki su tayata murnar Bude wannan Kamfanin.

Inda awajan anga yadda akewa jarumar make up wato kwalliya irinta zamani, Wanda anyi amfani da jambakin da jarumar take sarrafawa wajan yin kwalliyar Nata.

Saidai yadda jaruma Nafeesat Abdullahi tadanyi rawa awajan yayin yadda ake daukanta bidiyo hakan yasa nishadi a fuskokin masoyan jarumar kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon kasan.

Ga video

Nafisat Abdullahi acikin jarumai Mata na kannywood zamu iya cewar kusan Babu Wanda yakai jarumar dadewa a industry kannywood duba da irin shekarun data Kwashe acikin masana’antar.

Saidai bayan yadda Abubuwa Suka canja a masana’antar kannywood sanadiyyar karyewar tattalin arziki Wanda hakan yasa kasuwancin Fina finan ta ragu sosai, hakan yasa yanzu ba’a ganin manyan jaruman matan kannywood acikin Fina finai.

Duba da yadda Fina finan Hausa suka koma masu dogon zango Wanda ake nunasu akan manhajar YouTube inda anan masu Shirya Fina finan suke samun kudin shiga.

Wannan Dalilin yasa manyan jarumai Mata na kannywood suka koma harkar kasuwanci domin su tsira da mutuncinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button