Labarina season 4 episode 6 Gaskiya Baba Dan Audu yayi rashin imani awajan mutuwar Mahmud

Tabbas labarina season 4 episode 5 ya taba zuciyoyin mutane sosai duba da yadda mutane sukaita nuna fushinsu akan irin abinda baba Dan Audu ya aikata lokacin jana’izar Mahmud.

Domin baba dan Audu ya tabbata cikakken Mara Imani Kuma Mai son kudi domin mutane sukan tausayawa wajan mutuwa kokuma rashin lafiya. Saidai Shi baba dan Audu Mahmud Yana matsayin da awajansa amman Bai nuna damuwa akan mutuwar Mahmud dinba.

Labarina

Saidaima yadda yaje wajan mahaifiyar mahmud inda yaje ya karbo kudi domin Sayan likkafani ahakan ma dayaje shagon Sayan likkafani sanda yayi cuwa cuwa.

Makallata Shirin labarina seris suna ganin indai akace Mahmud ya mutu to Shirin labarina yazo karshe saidai wasu sunada shakkun cewar ba mahmud bane ya mutu domin har aka dauko gawa daga asibiti zuwa gida ba’a Nuno fuskar gawar ba, Kuma ance baba dan Audu yaje yayiwa Mahmud wankan gawa yace Bai iyaba.

Da wannan Dalilin wasu suke ganin kaman daraktan Shirin labarina yanas ya Wasa kwakwalwar masu kallon Shirin ne.

Acikin wata Hira da akayi da daraktan Shirin labarina Mal Aminu Saira gameda mutuwar Mahmud yace Shi bazaice komai ba domin film sirrine idan ya Fadi wani Abu dangane da mutuwar Mahmud to kaman ya fadawa mutane abinda zai faru nan gaba kenan.

Saidai yace makallata shirin labarina sucigaba da kallon domin tabbatar da mutuwar Mahmud dagaskene kokuma bada gaske bane iya abinda ya fada kenan.

Kucigaba da bibiyar shafinmu domin Samun labaran kannywood Dama wasu labaran cikin sauki Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button