Labarina season 4 episode 6 Matar Baba Dan Audu Ta Koresa Daga Gidanta Akan Abinda yayi lokacin mutuwar Mahmud

Labarina series shirine Wanda zamuce a dai dai wannan lokacin Babu shiri Mai dogon zango dayake daukar hankalin mutane kamarsa duba da irin salon yadda labarin yake tafiya.

Idan baku mantaba labarina season 4 episode 5 Wanda aka haska a ranar juma’a data wuce mutane sunga irin abun kunyar da baba Dan Audu ya aikata lokacin da ake kokarin jana’izar Mahmud.

Salon son kudi da baba Dan Audu ya yake nunawa acikin Shirin labarina yana matukar daurewa mutane Kai domin wasu masu kallo suna ganin cewar baza’a samu mutum Mai irin halin baba Dan Audu ba a wannan lokacin inda wasu Kuma suke ganin tabbas akwai Wanda sukafi baba Dan Audu son kudi a wannan zamanin.

Saidai kamar yadda kuke gani acikin hoton mahaifiyar mahmud ta kori baba Dan Audu daga gidanta, zamu iya cewar sabida irin rashin kirkin daya aikata lokacin rasuwar Mahmud yasa ta yanke shawarar gwanda ta Koresa tunda Dama gidantane ba gidansa bane.

Tabbas baba Dan Audu ya cancanci a Koresa Koko muce ya cancanci amai kowani irin hukunci domin ya nuna rashin Imani lokacin rasuwar mahmud acikin Shirin labarina season 4 episode 5.

Kucigaba da bibiyar shafinmu domin Samun cigaban Shirin labarina akoda yaushe Dama easy shirye shiryen Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button