Matar Bawa Mai kada Tacikin Kwanacasa’in Rahama MK Tayi Auren sirri

Wani labari daya fito daga shafin jaridar Demokaradiyya a Facebook da yammacin yau litinin 8 ga watan nuwambar shekarar dubu biyu da ashirin da daya jaruma Rahama MK Matar bawa mai kada tacikin shirin Kwanacasa’in Tayi auren sirri acikin wannan satin.

Rahama MK

A dai dai lokacin da makallata suke Zaman jiran dawowar Shirin Kwanacasa’in Mai dogon zango Wanda ake nunasa a tashar arewa24 kwata sai sukaji labarin auren matar Bawa Mai kada Rahama MK inda aka daura auren a ranar Asabar dinda ta wuce 6/11/2021 a birnin kano.

Jaruma Rahama MK tanada niyyar yin auren a lokacin baya Saidai cikin ikon ubangiji saiyanzu Allah yakawo Mata mijin, inda wannan auren anyisa cikin sirrine domin wasu daga cikin masana’antar kannywood din basusan da auren ba.

Wakilin jaridar Demokaradiyya yayiwa jarumar tambaya kamar Haka. Ya batun fitowa acikin shirye shirye
Amsa: eh zancigaba da fitowa acikin Shirin Kwanacasa’in na tashar arewa24 saidai sauran Fina finan ne banida tabbas gaskiya.

Kuma wannan aure danayi Ina rokon Allah ubangiji ya bani Zaman lafiya nida mijina, Ina rokon Allah ya azurtani da samun haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button