Babbar Kotu a Kano Ta Daure Mutumin Da Ya Kira Ganduje Da Barawo A Shafinsa Na Facebook

Kotun majistare dake zaune a Unguwar Nomansland a Kano ta daure wani magidanci bisa Kiran Gwamnan Jihar Kano D.r Abdullahi Umar Ganduje da Barawo a Shafinsa na Facebook.

An zargi magidancin mai suna Mu’azu magaji da cin zarafin gwamnan da kuma bata masa suna, kana da cin zarafin ‘ya ‘yan gwamnan Abdul’aziz Abdullahi ganduje da kuma Balara Abdullahi Ganduje.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta dai gurfanar da magidancin tare da wani Jamilu Shehu wanda yanzu tuni tuni Jamilu Shehu ya cika wandon sa da iska, a gaban Kotun bisa zargin Aikata Laifuka da suka hada da hada kai, tayar da hankalin Al’umma da kuma bata Suna.

A cewar kotun laifukan dai sun saba da Sashi na casa’in da bakwai (97) da na dari da goma Sha hudu (114) da kuma na Dari Uku da casa’in da Daya (391) da kuma na Dari Uku da casa’ib da tara (399) na kundin manyan Laifuka a Nigeria.

A cewar takardar ranar Ashirin da biyar (25) ga watan Oktoban 2021 Shugaban karamar hukumar Nassarawa ya kai kara sashin Leken Asiri na ‘yan sanda (SIB) inda ya shigar da korafi cewa wani mutum mai Suna Muazu Magaji Dan Bala, da Jamilu Shehu Dukkannin su mazauna karamar Karamar Hukumar Kiru dake Jihar Kano.

A ranar 25 ga watan oktoban ne dai Mutanen guda biyun suka sanya Hotunan Gwamnan Ganduje da ‘ya ‘yan sa Abdul’aziz ganduje da Bakaraba Suka Rubuta kuru-kuru karkashin Hotonsu “Barayin Kano” takardar ta kara da cewa shin ko kunsan wannan Abun da kuka yi Zai iya haifar da tarzoma a Jihar?

Sai dai ko da aka karantowa wanda ake zargin Laifukansa ya Musanta, wanda daga baya Lauyan sa ya roki kotu ta bayar da Belinsa.

Sai dai kotun taki amincewa ta bada belin wanda ake zargin sakamakon suka da Lauyan mai kara yayi wato Barr. Wada Ahmad.

Alkalin kotun mai Shari’a Aminu Gabari, ya umarci ofishin Binciken manyan Laifuka na rundunar ‘yan sandan Jihar kano ta bayar da kwafin Karar kafin kotu ta san wacce irin matsaya zata dauka, akan ko zata bayar da belin ko akasin Haka.

Daga Karshe dai mai Shari’a Aminu gabari ya dage Shari’ar zuwa Ranar takwas (8) ga watan nuwamban 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button