Duk Budurwa Mai Yawan Samari Allah yabata Miji irin baba Dan Audu cewar wani Saurayi

Biyo Bayan irin rashin mutuncin da baba dan Audu ya aikata acikin Shirin labarina season 4 episode 5 Wanda hakan ya matukar batawa mutane dayawa Rai.

A gefe guda Kuma Wani Saurayi a dandalin Facebook yayi wata addu’a ga yan Mata inda yake cewar duk macen datake yawan Tara samari Allah yabata Miji irin baba Dan Audu.

Wannan addu’ar dai saurayin yayita aikin Raha Dakuma alamar Dariya Wanda hakan Yana nuni dacewar yayi hakanne domin nishadi kawai Bawai dawata manufa.

Saidai zancen saurayin yazama abun mahawara a shafin sada zumunta inda Mata sukaita nuna rashin jindadin wannan kalaman saurayin duk da kuwa yayisa cikin nishadi ne Bawai Yana nufin hakan har cikin zuciyarsa ba.

Shirin labarina Yana dada samun karbuwa awajan matane duba da yadda salon labarin yake canjawa akoda yaushe yadda dan kallo bazai taba sanin mezai faru a episode nagababa.

Kucigaba da kasancewa da shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai Dama bidiyoyi cikin sauki Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button