Innalillahi Zan fita daga addinin Musulunci saboda ban ga amfaniN sa ba—Abba

Wani matashi ya bayyana cewa, “tun ina yaro nake cikin addinin musulunci amman har yanzu ban san amfanin sa, saboda haka zan fita daga cikin sa~Inji Matashi Abba Jigawa

Matashi Abba dan asalin jihar Jigawa ya bayyana cewa nan da sati daya zai bar addinin matukar al’ummar musulmi basu kawo masa dauki ba, duk kuwa da cewa bai bayyana irin dauki da yake bukatar a kawo masa ko kuma al’ummar musulmin su kawo masa ba.

Abba jigawa

Amma dai wasu na tunanin cewa wata kila matashin mai suna abba ya rasa na kashewa ne babu mamaki kudi yake bukata a bashi shi yasa yayi wannan barazana kamar yadda jaridar sokoto online ta rawaito.

Saidai ganin wannan labarin yasa mutane da dama sunyita tofa albarkacin bakinsu, inda suke bayyana cewar musulmin kwarai mumini bazai taba furta wannan kalmar ba domin haramunce.

Cikakken musulmi dolene ya yadda da kadda Wala maikyau kokuma Mara kyau wannan ma Yana daya daga cikin imani, saidai yanayin yadda Muka tsinci kanmu a wannan lokacin karancin ilimun addini shine yake haifar da wannan babbar matsalar.

Mungode da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint dakukeyi akoda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button