Badon Nayi Suna Nake Yabon Annabi ba Inji Stephanie Tacikin Shirin Dadinkowa

Dangane da yabon Annabi da jarumar kannywood Stephanie Wanda take taka rawa acikin Shirin Dadinkowa Wanda ake nunawa agidan talbija na tashar arewa24 tace badon tayi suna take yabon Annabi Muhammad s.a.w ba.

Stephanie

Yabon Annabi da Stephanie tayi a kwanakin baya Wanda duk da takasance ita Kirista ce yasa mutane suna fadin domin tayi suna takeyi inda wasu suke fadin cewar domin tasamu masoya yasa tayi hakan.

Saidai awata Hira da gidan jaridar VOA jarumar ta bayyana cewar ita Bawai tayi yabon Annabi domin tayi suna bane kokuma domin Samun masoya.

Stephanie Tace duk Wanda ya tsinci Kansa acikin musulunci kokuma kiristanci Bawai yin Kansa bane domin kuwa Kowa duk Wanda ya tsinci Kansa a musulmi ko Kirista Bawai shine ya zabama Kansa hakan ba Allah ne yazabamai hakan.

Stephanie takara dacewar ita duk musulmi da Kirista indai masoyinta ne tana kaunarsa Kuma tana girmama Kowa Kuma tana girmama addinin musulunci sosai kamar yadda take girmama addinin Kirista.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button