Anci Gaba da Shari’ar Hafsat Idris akan karban kudin wani kamfani miliyan daya datayi Bata musu aiki ba

Wata babbar Kotun jaha Dake lamba 18, Dake zamanta a garin Ungoggo karkashin Mai Shari’a zuwaira Yusuf tacigaba da Shari’ar jarumar masana’antar kannywood hafsat Idris Wanda Kamfanin UK Entertainment Suka shigar da Kara akan jarumar Kan kin karasa musu aikin dasuka bata.

Wakilin Dala FM Abubakar sabo ya rawaito cewar Kamfanin Yana karar jaruma Hafsat Idris akan sunyi alkawari Zata musu wani aikin (TV SHOW) na naira miliyan daya da dubu dari uku, saidai kafin a karasa aikin jarumar ta gudu.

Kamfanin UK Entertainment sunce bayan tafiyar Hafsat Idris sunyi kokarin tadawo akarasa aikin Amman Saidai jarumar Bata dawo ba wannan Dalilin yasa Kamfanin Suka yanke shawarar Kai karar jarumar gaban alkali.

Kamfanin UK Entertainment sunbukaci jaruma Hafsat Idris data dawo musu da kudinsu naira miliyan daya da dubu dari uku, sannan ta biyasu (Damages) naira miliyan goma.

Saidai wakilin gidan radio Dala FM ya rawaito cewar ranar farko da akai Zaman a kotu jarumar Bata halatta sannan Bata Aiko dawani ya wakilce taba kokuma wani sakon dalilinta na rashin zuwa Kotun.

Saidai a Zaman Kotun da akayi jarumar ta turo wani lauyanta maisuna Usman kabara inda lauyan jarumar ya shigar da takurdun Kare jarumar agaban alkali.

Saidai yanzu wannan karar an dagata zuwa watan gobe takwas ga watan goma Sha biyu kenan Wanda yayi dai dai da 8/12/2021 inda ranar za’a gabatar da shaidu na dukkan bangarorin guda biyu domin Jin tabakinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button