Hadiza Gabon tayi wani bayani Kan Mutuwar Mahmud nacikin Shirin Labarina

Hakika Shirin Labarina na Kamfanin Saira Movies Wanda yake zuwa agidan talabijin na tashar arewa24 yazo da sabon salo, inda aka Nuno mutuwar Mahmud Dakuma batar Sumayya.

Inda Mahmud ya mutu gakuma Tashin hankalin da mahaifiyar Mahmud da abokinsa Umar Suka shiga, inda agefe guda Kuma mahaifiyar sumayya, rukayya da lukman suka shiga Tashin hankalin a lokacin da sumayya itama aka nemata aka rasa.

Labarina season 4 episode 5 yasa mutane sunta tofa albarkacin bakinsu Dakuma wasu daga cikin jaruman kannywood. Inda wasu suke ganin da wahala ace Mahmud ya mutu acikin Shirin tunda haryanzu ba’a Nuno fuskar gawar Mahmud ba.

Sanadiyyar yadda mutane suketa tafka muhawara akan mutuwar Mahmud acikin Shirin labarina yasa gidan radio muryar amurka ta tattauna da daraktan Shirin labarina kamar yadda Muka kawo muku.

Yanxuma dai jarumar kannywood Hadiza Gabon tareda shahararren Dan kwallon kafar najeriya Shehu Abdullahi Suka tattauna akan Shirin labarina ta hanyar bidiyo call.

Hadiza Gabon Tace: idan anga Dama anan gaba za’a iya cewa Mahmud Bai mutu ba yananan a raye, inda tabada misali da wani film da aka tabayin hakan acikinsa.

Makallata Shirin labarina haryanzu Basu gamsu da hujjojin da aka bayar kan Mutuwar Mahmud ba domin kuwa ba’a Nuno gawar Mahmud dinba haryanzu.

Kucigaba da bibiyar shafinmu domin Samun labarai cikin sauki Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button