Labarina season 4 Shin ya kuke Ganin presidor zaiji idan yaji labarin batar Sumayya

Shirin labarin seris Yana matukar daukar zafi inda zamuga mahimman Abubuwa guda biyu dasuka faru acikin season 4 episode 5 Wanda na farko shine Mahmud ya mutu na biyu Kuma shine sumayya ta Bata.

Acigaba da kokarin da Saira Movies sukeyi wajan kawo muku cigaban labarina series Wanda yanzu Haka suna garin Kaduna inda suke daukan sauran aikin labarina season 4.

Hakanne yasa Tashar Latest Hausa tayi tattaki harzuwa inda ake daukar wannan karashen Shirin labarina domin tayi Hira da isah feroz kha Wanda kukafi sani da presidor acikin Shirin labarina kamar yadda zaku gani a wannan bidiyon.

Ga video

Saidai alamu suna nuni da cewar tabbas akwai Abubuwa Wanda zasu faru nan gaba duba da irin mutuwar Mahmud da bacewar sumayya.

Haryanzu wasu daga cikin makallata Shirin labarina Basu yadda cewar Mahmud ya mutu. Domin gani suke indai akace Mahmud ya mutu to Shirin bazaiyi Dadi kamar yadda yakeyi a yanzu Haka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button