An Karrama Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Matsayin Gwarzon shekara a Kasar India

A ƙasar India An karrama Sanata kwankwaso amatsayin gwarzon daya tallafawa harkokin ilmi.

Mataimaki na musamman ga Sanata Rabiu kwankwaso Hon Saifulllahi Mohd ya rubuta kamar Haka Yana Cewa A matsayin wanda ya tashi tsaye kuma ya jagoranci harkar ilimi da Dimokradiyya, an gayyaci Mai girmaJagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yau (13th November, 2021) zuwa Jami’a Swarrnim Startup and Innovation University, a garin Gujarat dake India.

A cikin tawagar sa akwai Engr Abubakar Sadiq, Mazi Odinaka Chukwu da Mr Sandeep Bhatia. Sun zagaya jami’ar kuma an nuna musu kayan aiki da al’adun kasar. Jami’ar itace ta farko a kasar India wadda ta fuskanci fannin raya masana’antu da kirkiran abubuwa na fasaha. Garin Gujarat shine garin Mahatma Ghandi da kuma Firimiya (Prime Minister) na yau Shri Narendra Modi na kasar India.

Sanata Rabi’u Musa kwankwaso ya Kasance mutun na ‘daya a Nageriya wajen daukar nauyin karatun ‘ya ‘yan talakawa Zuwa kasahen duniya daban daban ciki harda kasar ta India domin Karo karatun Zamani harda na Addinin Islama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button