Mal Ali Nacikin Shirin Kwanacasa’in Yayi Kuka da Hawaye Kan Irin Masifar Da Talakan Najeriya Yake ciki

Biyo bayan matsalolin dasukai yawa a fadin najeriya Wanda zamu iya cewar matsalar tsaro itace babban Abu Wanda ta addabi Kowa da Kowa Wanda hakan yasa mawakan Hausa sukeyin wakoki domin Jan hankalin gwamnati.

Musamman idan Muka dawo gefen arewacin najeriya yadda matsalar tsaro da satar mutane tayi yawa Wanda hartakai daliban makaranta ana binsu har makarantun su ana daukesu domin Neman kudin fansa.

Mal Ali Nacikin Shirin Kwanacasa’in shima yazo da tasa wakar inda yayi wakar cikin Kuka tareda bayyana wasu kalamai masu karya zuwciya dakuma bayyana irin halin da talaka yake ciki Dakuma halin da Yan Arewa suke ciki.

Ga video

A kwanakin baya naziru sarkin Waka da Ali jita da fresh emir sunfitar da Waka akan irin wannan matsalar data addabi arewacin najeriya Dama najeriyar baki daya.

Shima Mal Ali Nacikin Shirin Kwanacasa’in yabi sahun mawakan inda shima yayi wakar akan matsalar datake demun talakawan najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button