Masha Allah Kalli Yadda jaruma Mansurah isah take bi gida gida tana Rabon abinci kyauta

Masha Allah tsohuwar jarumar kannywood Mansurah isah tanabi gidaje gidaje inda ake taimakawa mabukata da Kayan abinci acikin garin Kano.

Inbaku mantaba dai tsohuwar jarumar tanada wata kungiyar Wanda suke tallafa marayu da gajiyayyu da taimakon abinci Dakuma taimako dasuka shafi rashin lafiya da sauransu.

A yammacin yaune Sha uku ga watan nuwambar shekarar dubu biyu da ashirin da daya jarumar ta wallafa wasu hotunanta a shafinta na Instagram inda akaga jarumar tareda abokan aikinta sunabi gidaje gidaje suna Rabon abincin ga mabukata.

Mansurah isah da Fauziyya D Sulaiman suna daya daga cikin matan dasukai suna wajan taimakawa mutane acikin arewacin najeriya Wanda dukkansu sun kasance mazaune garin Kano.

Wanda Matar maigirma shugaban Kasa muhammadu buhari Tasha turo musu da Kayan abinci domin rabawa mabukata Haka zalika manyan Yan kasuwa da manyan ma’aikatan gwamnati sukan turawa kungiyoyin Kudade domin su rabawa mabukata da marasa lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button