Allah ne ya dorawa Maryam Yahaya rashin lafiya ba Yan kannywood ba

Maganar rashin lafiyar jaruma Maryam Yahaya abindai Yana sake daukan sabon salo domin Kowa da irin abubuwan dayake fada akan rashin lafiyar jarumar.

Saidai shugaban Kamfanin tace Fina finai na Jahar Kano Ismail na’abba afakallu yayi tsokaci dangane da rashin lafiyar Jaruma Maryam Yahaya Wanda mutane suketa cewar Yan kannywood sunyi watsi da jarumar.

Yace rashin lafiyar Maryam Yahaya cutane daga Allah bawai mune muka daura Mata ba domin Babu Wanda ya Isa ya daurawa wani rashin lafiya face Allah daya halicce mu Dan Haka baikamata ace mutane suna zagin Yan Hausa film ba akan rashin lafiyar jarumar.

Bugu da Kari dukkan jarumai maza da Mata nacikin masana’antar kannywood sun matukar shiga damuwa akan rashin lafiyar Maryam Yahaya sannan suna zuwa har gida suna duba jarumar.

Afakallu ya Kara dacewar mutane suna fadin abinda Basu saniba akan rashin lafiyar Jarumar Wanda laifin suna daurawa Yan kannywood Wanda hakan baikamata ba domin kuwa badai dai bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button