Mata biyu a kannywood sun ishemu ishara inji Director Sunusi Oscar 442

Wata magana da daraktan Shirya Fina finan Hausa yayi sunusi Oscar 442 ta a shafinsa na Instagram inda maganar jarumin ya taba zukatan masoyan nasa.

Inda daraktan ya Rubutu kamar Haka a shafinsa na Instagram kamar Haka “Mata biyu a kannywood sun ishemu ishara” wannan maganar da daraktan yayi yasa mutane suke fadin cewar matan sune Maryam yahaya da zainab indomea.

Idan muka tuna baya zamuga yadda daukakar jaruma zainab indomea ta gushe acikin masana’antar kannywood lokaci daya duba da irin yadda jarumar tayi tashe wanda Saida takasance itace jarumar datafi kowace jaruma suna da samun kudi da masoya a lokacin Nata saidai Kuma yanzu Bata masana’antar.

A dayan bangaren kuma idan Muka duba yadda Rayuwa tayi da jaruma Maryam yahaya duk wani Wanda yake bibiyar shafukan sada zumunta Yasan labarin rashin lafiyar Maryam Yahaya data shafe wata hudu tana fama dashi.

Saidai a yanzu jaruma Maryam yahaya tafara samun lafiya inda ta wallafa bidiyon ta a shafinta na tiktok Wanda ta daukesu acikin wani falon alfarma.

Amman haryanzu Maryam yahaya Bata dawo harkar Fina finan Hausa ba sakamakon Bata Gama samun cikakkiyar lafiya ba. Muna rokon Allah ubangiji ya Bata lafiya da sauran Musulman Duniya Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button