Shigata kurkuku Ya batamun tarihin rayuwata – cewar Jarumi Adam a zango

Cikin wata Hira Wanda gidan BBC Hausa sukeyi da jaruman kannywood maisuna “daga bakin Mai ita” Adam a zango ya bayyana cewar shigarsa kurkuku ya Bata mishi tarihin rayuwarsa.

Idan baku mantaba Jarumi Adam a zango shine Jarumi na farko da hukumar Tace Fina finai ta aikashi gidan yari a shekarar 2007 karkashin jagorancin Abubakar Rabo sakamakon wani Album da Adam a zango ya saki maisuna Bahaushiyasa a lokacin.

Haka zalika Jarumi Adam a zango ya bada labarin wata budurwa Wanda a lokacin tana matukar sonsa shikuma Yana nuna Mata halin ko inkula ma’ana Shi baya sonta. Inda daga baya Soyayyar ta jiya a inda Adam a zango yadawo yanason jarumar ita Kuma Bata sonsa.

Haka zalika cikin hirar jarumi Adam a zango ya bayyana cewar dazarar yasamu wata sana’ar datafi harkar wasan Hausa zaibar wasan Hausan, cewar jarumin. Gadai cikakkiyar bidiyon da akayi da Jarumi Adam a zango kuji daga bakinsa

Ga video

Baya ga Haka Jarumi Adam a zango ya bayyana yadda yaransa sukemai butulci bayan yagama rainonsu sunkai wani mataki a rayuwa. Sai daga baya Kuma sugane sunyi kuskure sudawo wajan nasa tareda basa hakuri domin acigaba da zama kamar yadda ake ada.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button