Mama Saratu Daso ta bude Katafaren wajan shagalin biki,suna da walima maisuna Daso Event Center

Uwa acikin masana’antar kannywood Wanda ta shafe sama da shekara goma Sha biyar acikin masana’antar kannywood Saratu Gidado Wanda akafi sani da Mama Daso ta bude sabon wajan shagalin biki acikin birnin kano.

Mama Daso itama tabi sahun sauran jarumai maza da Mata wajan Kama wata sana’ar sakamakon karyewar tattalin arzikin masana’antar kannywood Wanda ya janyo kasuwancin Fina finai a kannywood yayi Kasa sosai.

Sanadiyyar karayar tattalin arzikin masana’antar kannywood din yasa jarumai Mata Suka koma harkar kasuwancin Saida kayayyakin sawa, takalma, Kayan kwalliya da sauransu.

Ga video shagalin bikin bude wajen taron

Mama Daso ta gayyaci Yan uwa da abokan arziki da Yan uwan sana’arta na kannywood domin suzo su tayata Farin cikin wannan waje data bude. Inda anga manyan jarumai awajan kamarsu Hadizan saima, baban chinedu, Hauwa waraka, Aysher Humairah, Fatee slow, Dauda kahuta rarara.

Ciki Harda shugaban hukumar Tace Fina finai na kannywood wato Ismail na’abba afakallah tareda wasu jiga jigai acikin masana’antar kannywood. Muma daganan shafin Arewajoint Muna taya mama Daso murnar Bude wannan waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button