Sabuwar Soyayya ta barke tsakanin Sani Musa Danja da jaruma Rahama Sadau

Wani sabon hotunan jaruma Rahama Sadau da sani Musa Danja kenan dasuketa yawo a kafofin sada zumunta inda akaga jarumar cikin shigar fulani tareda sani Danja.

Wata sabuwar Soyayya ce ta barke tsakanin jaruman guda biyu saidai wannan Soyayyar acikin wani sabon shiri da ake dauka maisuna “GAMBO DA SAMBO” da ake Kan dauko.

Shirin SAMBO DA GAMBO wani sabon shirine Wanda ake dauka a yanzu Haka a Jahar adamawa Wanda film din da yaren turanci zaizo muku ma’ana English.

Idan baku mantaba itadai jaruma Rahama Sadau yanzu an dakatar da fitowarta acikin Fina finan Hausa sakamakon laifin data aikata a shekarar data wuce.

Bayan dakatar da jarumar ne Takoma fitowa acikin Fina finan kudancin najeriya wato (Nigerian film) kasancewar Shima kamfanine Mai Zaman Kansa Kuma basuda Shari’ar musulunci acikinsa.

Wannan shine babban Dalilin Dayasa aka daina ganin jaruma Rahama Sadau acikin sababbin Fina finan Hausa dasuke fitowa a halin yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button