Gaskiyar Magana Muna Matukar Bukatar Aure a wannan lokacin Jamila Nagudu da Rashida Mai Sa’a

Fitattun jaruman kannywood guda biyu Wanda sun shafe sama da shekara goma Sha biyar acikin masana’antar kannywood suna Neman mijin aure Wanda yake sonsu tsakani da Allah wato Jamila Nagudu da Rashida Mai Sa’a.

Jaruma Rashid Mai Sa’a ta bayyana cewar duk wani Wanda ya Shirya aure Kuma yake sonsu tsakani da Allah Suma a shirye suke dasu soshi domin a daura musu aure.

Rashida Mai Sa’a tace to jama’a kusani Ni Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a da kawayena su Hadiza kabara dasu Teema yola da Jamila Nagudu duk cikakkun zawara ne idan akwai Mai son wata acikinmu Kuma ya shirye to yafito muma a shirye muke.

Kuma duk Wanda yafito Zan tsayamai a matsayina na shugabarsu dan Haka idan har da Mai bukatar aurenmu to yafito a shirye muke tsakaninmu da Allah.

Saidai wasu suna ganin abinda tsohuwar jarumar Tafada Rashida Mai Sa’a wasane ba gaske bane domin idan dagaske suna Neman mijin auren bazasu rasa ba Kuma basaima sunzo kafofin sada zumunta sunyi tallan kansu ba.

Saidai a wannan zamanin indai mace tanada kudi komai tsufanta Zata iya samun saurayin dazai aureta Haka zalika shima namiji duk tsufansa indai yanada kudi zaisamu macen dazata auresa Kuma tazauna dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button