Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Halinda Rukayya Labarin take ciki na rashin lafiya
Fitacciyar jarumar kannywood Teema yola Wanda akafi sani da rukayya kawa ga sumayya acikin Shirin labarina Mai dogon zango na tashar arewa24 batada lafiya.
Cikin wani gajeran bidiyo da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram inda cikin bidiyon munga jarumar kwance ana kara Mata ruwa akan Gadon asibiti tareda Yan uwanta a gefenta.

Saidai jarumar Bata bayyana abinda ya janyo Mata rashin lafiyar ba, Haka zalika Bata bayyana sunan asibitin datake kwance ba kamar yadda masoyan jarumar Suka bukaci Tafada musu sunan asibitin domin suzo su gaisheta
Rukayya tana daya daga cikin jarumai Mata Wanda suke tashe acikin masana’antar kannywood. Rukayya takara samun daukaka tareda Kara samun masoya sanadiyyar Shirin labarina.
Duba da yadda tafito a matsayin kawa tagari Mai tsoron Allah, Wanda Zata iya Kare mutuncin kawarta sumayya akowani irin Yana acikin kowani irin Hali wannan Dalilin yasa jarumar takara shiga zukatan masu kallon Fina Finan Hausa.