Jarumar kannywood Ummi Rahab tasai sabuwar waya kirar iPhone 13 Naira 800,000

Ummi Rahab tana daya daga cikin jarumai Mata na kannywood dasuka Fara Sayan waya kirar iPhone 13 Wanda itace wayar datafi kowace waya daukar hankali a idon Duniya.

Inda jarumar ta wallafa wani gajeran bidiyo a shafinta na Instagram inda take godewa Allah bisa wannan kyautar dayayi Mata, Haka zalika ta wallafa hotunanta rike da wayar a hannunta.

Ummi Rahab

Saidai ganin yadda wannan wayar take da tsada yasa mutane suka Fara cece kuce akan cewar jarumar ae batada kudin sayan wannan wayar domin bawata Sana’a takeyi ba.

Inda wasu suke fadin cewar ai rike waya badole saikana da Sana’a zaka rike domin jarumai irinsu Ummi Rahab za’a iya Basu kyautar wayar datafi iPhone 13 tsadama.

Saidai biyo Bayan wallafa cewar tasai iPhone 13 a shafinta na Instagram wato Ummi Rahab bayan kwana biyu anga wasu jarumai Mata nacikin masana’antar kannywood din Suma sunafara wallafa hotunan nasu tareda sabuwar wayarsu kirar iPhone 13.

Inda wasu suke zargin jaruman Mata suna gasar wayoyi tsakaninsu kenan domin kuwa hakan ta taba faruwa lokacin da iPhone 12 tafito inda wasu Mata acikin masana’antar sukai gasar wayar Wanda harsai datakai masoyan jaruman sungane cewar suna gasar wayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button