Wallahi Duk Wani Mai Shirin yin Aure Ya Tsaya Ya Kalli wannan bidiyon innalillahi

Cikin jawabin da shehin malamin yakeyi ga Wanda suke da niyyar aure malamin ya bayyana cewar idan za’ayi auren anaso namijin yafi mace da Abubuwa guda uku sannan itama macen anaso tafi namijin da Abubuwa guda uku sannan su hadu akan Abu guda uku.

  1. Gefen Ango anaso yafi matarsa Abu guda uku: Shine yazamana ka girme matarka a shekaru. Sabida gudun samun matsala irin na matan zamani wata idan taga tagirme mijin to raini zaishiga tsakaninsu. Amman inma ka auri Matar data girmeka ahakan ma ba matsala bane.
  2. Na biyu shine yazamto kafi matarka ilimin addini sabida hakan zai infants Zaman auren naku Sosai da sosai domin wajan karantar da ita dadai sauransu.
  3. Abu na uku shine kafi matarka Dukiya wannan ma Yana daya daga cikin abubuwan dazasu saka Zaman aure yakara inganci. Domin idan ka auri macen data fika kudi tabbas akwai yiwuwar samun matsala acikin zamantakewar auren naku.

Ga video shehin malamin

A gefen Amarya Kuma anaso tafika Abu uku sune

  1. Tafika karancin shekaru wannan ma Yana daya daga cikin abubuwan dazasu sa asamu ingantaccen Zaman aure tsakanin Ango da amaryarsa.
  2. Na biyu shine yazamto Matar taka tafika kyau a cewar malamin. Eh yawanci a cewar mutane matan sunfi maza kyau inda wasu Suka Suma bayyana cewar maza sunfi Mata kyau.
  3. Sannan Abu na uku shine yazamto a gefen soyayyar taku ita macen tadan fi Sonka da “Kadan” akan yadda kake Sonta wannan ma Yana inganta Zaman aure.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai da dumi duminsu Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button