Innalillahi Adam a zango da Ado Gwanja sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Nijar

Wani mummunan lamarin daya faru da jaruman kannywood guda biyu Adam a zango da Ado Gwanja akan hanyarsu ta zuwa nijar inda direban motarsu ya bige wata Mata.

Rahotanni sun bayyana cewar direban nasu ya bige wata Mata akan hanyarsu ta zu a nijar inda sunma Shiga cikin nijar suna daf da zuwa masaukinsu Suka bige wata Mata tareda yaranta inda anan take Allah ya karbi ran Matar tareda yaranta guda 3.

Saidai bayan faruwar wannan alamari jami’an tsaron kasar nijar sunkam direban su ado Gwanja da Adam a zango.

Wata mazauniyar kasar nijar tafito ta nuna irin takaicin abinda jaruman guda biyu Suka aikata inda take fadin Cewar: duk da cewar abinda ya faru tsautsayi ne Amman baikamata ace Adam a zango da Ado Gwanja sun halarci bikin da aka gayyacesu ba Yakamata su hakura da zuwa bikin.

Acewarta jaruman sun nuna halin Rashin kulawa inda sukatafi wajan shagalin bikin da aka gayyacesu a maimakon sutafi gidan Yan uwan Matar dasuka bigeta da yaranta Suka rasu domin nuna alhinin abinda ya faru.

Gawani cikakken videon domin kugani

Akwai rahotannin dasuke yawo a kafofin sada zumunta cewar ankama Jarumi Adam a zango da Ado Gwanja inda an kullesu a kasar nijar. Saidai wannan labarin ba gaskiya bane.

A halin yanzu dai jaruman suna cikin koshin lafiya direbansu Kuma Yana hannun hukumar tsaron kasar nijar kafin zuwa lokacin dazasu Gama Bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button