Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah yayiwa Mahaifin Jarumi Umar Gombe Rasuwa

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un a jiyane da yamma Allah ya karbi ran mahaifin daya daga cikin jaruman kannywood Umar Gombe da yammaci.

Jarumi Umar Gombe ya wallafa wani gajeran Rubutu a shafinsa na Instagram inda ya rubuta “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah yayiwa mahaifina rasuwa za’ayi jana’izar sa gobe a fadar sarkin Gombe da misalin karfe goma na safe”.

Ganin wannan sakon mutuwar ya tashi hankalin jaruman kannywood inda kamar sarki Ali Nuhu shima ya wallafa hoton mahaifin jarumin tareda rubuta Allah ubangiji yaji Kansa da Rahama.

Jaruman kannywood maxansu da matansu kamarsu Falalu a dorayi, Ali jita, ado Gwanja, Abubakar Bashir maishadda, Teema yola,Aysher Humairah, Hadiza Gabon da sauransu suntaya jarumin alhinin mutuwar mahaifin nasa.

A yanzu Haka ana Zaman karban gaisuwa a can gidan mahaifin jarumin a Jahar Gombe. Muna rokon Allah ubangiji ya gafarta Masa yasa ya huta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button