Shin dagaske Rahama Sadau tadawo film ne bayan korarta da akayi a shekarar 2020

Shin dagaske jaruma Rahama Sadau tadawo film ne itace tambayar da makallata Shirin wasan Hausa sukeyi, tun bayan bayyanar hotunan jarumar acikin wani sabon Shirin barkwanci maisuna “Gambo da Sambo”

Wanda ake dauka a garin Gombe Wanda Shirin ya kunshi jaruman kannywood irinsu magaji mijin yawa, Rahama Sadau, Rabiu Daushe da sani Musa Danja.

Ganin ana daukar Shirin awata jaha dake jahohin arewa Kuma tareda wasu jaruman kannywood hakan yasa wasu suke tambayar ko jaruma Rahama Sadau tadawo masana’antar kannywood ne da Shirya film.

Sanin kowane abinda ya faru da jarumar a shekarar data gabata Wanda akasha dambaruwa tsakaninta da abokan sana’ar nata harma da sauran alumma masoya Annabi bayan bayan shigar datayi akai rashin sa’a wani fajiri ya taba martabar Annabi Muhammad a kasan hoton Nata.

Wannan lamari ya tada Kura matuka Wanda hartakai kungiyar mashirya Fina finai ta Kasa moppan sun bada sanarwar dakatar da jarumar a Karo na biyu duk da tafito tayi kuka bada hakuri.

Saidai kawo iyanzu Babu wata sanarwa a rubuce kokuma a aikace Wanda take bayyana korar da akayiwa jarumar kowani Abu maikama da hakan. Wanda itama jarumar ba’a Kara ganinta awani shiri ba hatta da shirinta datakeyi Mai dogon zango maisuna “Yar minista” Wanda take haskawa a tasharta ta YouTube ta dakatar dashi.

Saidai bayan wannan anga jarumar tacigaba da Fina finan kudancin kasar najeriya wato Nollywood inda tafito awani shiri Mai dogon zango maisuna “The Plan” Jim Kadan Bayan faruwar lamarin. Bama iyanan ta tsaya ba jarumar tasamu damar ketare hazo izuwa kasar India inda aka dauki Shirin “khuda Haafiz” zango na biyu da ita.

Sai a wannan Karon aka ganta a garin Gombe cikin jaruman kannywood tana daukar Shiri Amma Koda mukayi bincike duk da a arewacin najeriya ake daukar Shirin. Shirin bana Yan kannywood bane nawani fitaccen Mai Shirya film ne a kudancin kasar maisuna Dimbo Atiya Wanda shine mashiryin Shirin Nan na “Son of the khalifate”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button