Tabbas abinda Ali Nuhu ya fada ya matukar girgiza kannywood innalillahi

Jarumi Ali Nuhu ya kasance babban Jarumi acikin masana’antar kannywood Wanda duba da yadda yabada gudunmawa Dakuma dadewa acikin kannywood yasa ake kiransa da sarki Ali Nuhu.

Cikin wani Hira da akayi da Jarumi Ali Nuhu ya bayyana wasu abubuwa Wanda mutane suka Dade suna rokon jarumin akan yakamata ya dainasu domin girma ya kamasa.

Tambayar da akayima Ali Nuhu shine shin yaushe zaka daina rawa?

Eh tabbas yanzu Duniya ta canja duba da yadda yanzu Matasa suke bada kwazo wajan yin rawar ba kamar zamanin baya ba. Kuma yanzu yawancin Fina finan Hausa zakaga idan za’ayi rawa ana dauko Yan rawa.

To yanzu a zahirin gaskiya yanzu nadaina yin rawa acikin film inji Ali Nuhu, hakan na nufin Bawai na daina rawa kwata kwata bane. A’a zanyi Dan rawa Amman batareda da Yan rawa ba, saidai Ni kadai Wanda zanyi rangaji Dakuma juyi dai Haka.

Ali Nuhu ya Kara da cewar yanzu Mun barwa ya’yan mu Dakuma kannenmu rawa duba da yadda shekaru Suka kamani yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button