Wallahi Bazan iya Auren Alawaiyya Ta Dadinkowa Ba Ko a zahiri – cewar Nazir nacikin Shirin Dadinkowa

Cikin wata Hira Wanda gidan jaridar BBC Hausa suke gayyatar jarumai maza da mata daga cikin masana’antar kannywood domin suyi Hira dasu Susan tarihinsu tareda yadda akayi suka Shiga harkar Fina finan Hausa.

A wannan Makon bakon da aka gayyata bawani bane illa Ahmadbello Wanda akafi sani da nazir acikin Shirin Dadinkowa Wanda yake zuwa muku duk ranar Asabar da misalin karfe takwas na dare a gidan talbijin na arewa24.

Daga cikin tambayoyin da akayiwa jarumin sun hada da awani gari aka haifesa a Ina yayi karatu Dakuma inda ya girma sannan da yadda akayi yashiga harkar wasan Hausa.

Ga video

Ahmadbello ya bayyana cewar cikakken Dan garin Jos ne Shi yayi primary da secondary dukka a garin Jos sannan ya wuce jami’a (University) duk a garin Jos din kamar yadda kukaji acikin hirar.

BBC Hausa sun tambayi jarumin wace tambaya masoyansa sukafi yimai?

Nazir yace tambayar da akafimai itace Ina Alawaiyya saidai a zahirin gaskiya mutane suna tunanin auren damukayi da Alawaiyya auren gaskene. Wannan auren ba auren gaske bane domin duk abubuwan dasuka faru acikin Shirin ba gaske bane kirkirarren labari ne kawai.

A yanzu hakama mutane dayawa basusan cewar Alawaiyya tayi aure na Kuma har Allah ya azurtata da samun haihuwa Dan Haka Babu zancen aure tsakanina da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button