Wata sabuwa Har yanzu ban samu mijin da ya dace na aura ba inji Adama Matar Kamaye

Fitacciyar jaruman nan kuma wacce ta yi suna a cikin shirin nan mai dogon zango na “Dadin Kowa”, Hajiya Zaahra’u Sale wacce aka fi sani da Adamar Kamaye.

Jarumar ta bayyana burin da take dashi na yin aure, a kowanne lokaci matukar ta samu irin mijin da take mafarkin samu a rayuwa.

Fitacciyar jarumar ta sanar da haka ne a wata hira da tayi da jaridar Dimukaradiyya, inda suke tambayar ta ko tana da sha’awar yin aure kuwa, ganin yadda shekarunta suka ja.

Adama ta ce:

“Ba ni da aure a yanzu, sai dai ina da niyyar yin aure, idan Allah ya kawo mun miji nagari zan yi aure. To Amma ka san su maza har kullum ba sa yi wa matan adalci, wani lokacin kuma matan ne ba sa yi wa mazan adalci, to amma ina son, duk wani mai kauna ta da masoyana, su taya ni da addu’a Allah ya ba ni miji nagari wanda za mu zauna lafiya ni da shi” inji ta.

Ina da niyyar aure, kullum a cikin niyyar nake. Amma dai har yanzu ban dace da kalar wanda zan aura ba, mu zauna da shi din ba ne, sai dai ana nan ana lalube kuma ana bai wa Allah zabi, ya zaba mana abin da ya fi alheri. Dan aure ai ba zai ki yin aure ba” a cewar ta.

Ta cigaba da cewa

”Don shi aure sunnar Manzon Allah ne, kuma duk Musulmi ba zai ki sunnar Manzon Allah S A W ba. ”

Da aka tambayeta ko za ta iya auren Kamaye, wanda ta fito a matsayin matarshi a shirin “Dadin Kowa”, Adama ta ce:

 “Ai shi Kamaye Ubangidana ne, don haka ina yi masa kallon Ubangidana ne, ba wanda zan aura ba, don ana maganar ko zan aure shi ko Malam Nata’ala, to gaskiya duk a cikin su ban ga miji aure ba. Abokan aiki na ne a harkar fim.

A karshe Zahra’u ta nuna sakon godiyar ta ga daukacin masoyanta da suke nuna mata ruwan kauna da addu’o’i, inda ta ce duka wannan daukakar da ta samu a rayuwa ta saboda masoyanta ne da kuma addu’ar da suke yi mata.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button