Ado Gwanja Yanaci Gaba Da Shan Zagi Sakamun Turawa Davido Kudi Dayayi

A jiyane laraba Sha bakwai ga watan nuwambar shekarar dubu biyu da ashirin da daya, 2021 inda shahararren mawakin kudancin najeriya Wanda Duniya ta Sansa “Davido” ya bayyana cewar zaiyi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa (Birthday).

Inda ya bukaci abokanansa Dakuma Wanda ya taimaka a rayuwarsu da Wanda sukejin dadin wakokinsa dasu hadamai gudunmawar naira miliyan daya N1,000,000 hakan zai tabbatar yanada masoya nagari kokuma bashida dashi.Inda a Karon farko cikin mintuna goma 10 yasamu naira miliyan bakwai N7,000,000 inda daganan aboknan mawakin sukaita turamai kudi.

Saidai a yaune akaga shaidar mawakin arewacin najeriya Wanda yake zaune a garin Kano Ado Gwanja shima yana daya daga cikin Wanda suka turawa da mawaki Davido Kudi, inda Ado Gwanja ya tura da naira dubu goma N10,000 a matsayin tasa gudunmawar.Saidai tun bayan bayyanar shaidar alamar ado Gwanja ya turawa da mawaki Davido Kudi yake Shan Suka da zagi da dandalin sada zumunta.

Inda wasu suna ganin jarumin baikamata ace ya tura wannan kudi ba duk da kudin basuda yawa kamar yadda mutane suke fada.Masoyan Ado Gwanja sun bayyana cewar dubu goman daya turawa da mawakin da dauka yayi yabawa mabukata sadaka dasai tafimai alheri acikin rasuwarsa Duniya da lahira.

Sun bayyana cewar mawaki Davido yanada arziki Kuma mahaifinsa shima yanada arziki Amman Neman suna shine yasaka mawakin ya turamasa da kudi alhalin akwai mabukata almajirai marasa lafiya dasuke da bukatar kudin a inda mawaki Ado Gwanja yake.Inda wasu daga gefe guda Kuma suke ganin abinda mawakin yayi dai dai ne domin Babu Wanda Yasan tsakanin mawaki Ado Gwanja da Davido Babu mamaki mawaki Davido ya tabayima Ado Gwanja wani abun alkairinne.

Mungode da bibiyar shafinmu dakukeyi akoda yaushe. ku Danna alamar kararrawar dakuke gani domin Samun labaranmu cikin sauki da zarar Mun daura Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button