Innalillahi Jarumi Lawan Ahmad (Umar Hashim) Yana Neman Taimako Daga wajan Masoyansa

Fitaccen Jarumi Lawan Ahmad Wanda kukafi sani da (Umar Hashim) acikin shirinku Mai Farin jini izzar so Yana Neman taimakon masoya Annabi Muhammad S.A.W dake fadin duniya gaba daya.

Jarumi Lawan Ahmad ya wallafa wani gajeran rubutu a shafinsa na Instagram da misalin karfe takwas na dare inda ya rubuta ” Nima Yau inaso inci albarkacin Annabi Muhammad s.a.w agun Masoyana” tareda saka lambar asusun bankinsa.

Wannan Yana zuwane bayan mawakin kudancin najeriya Davido ya bayyana cewar Yana neman naira miliyan daya domin zai gudanar da Shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa wato (birthday) dinsa inda ya bukaci abokanansa dasu kawo gudunmawa.

Hakan yasa mawaki Davido yafara samun miliyoyin Kudade cikin Kan kanin lokaci hakan ya bawa mutane mamaki domin acikin awanni gomasha mawaki Davido ya samu kudi kimanin naira miliyan dari da goma Sha Tara.

Hakan yasa wasu daga cikin jaruman kannywood Suma Suka Fara wallafa cewar sunaso masoyansu su nuna musu Soyayya ta hanyar tura musu Kudade asusun bankunansu.

Hakan yasa lawan Ahmad Wanda kukafi sani da (Umar Hashim) acikin izzar so shima ya wallafa hakan a shafinsa na Instagram inda ya bukaci masoya Annabi Muhammad dasu tura Masa kudi acikin bankin asusunsa.

Wannan wani sabon lamarine Wanda yaketa yawo a kafofin sada zumunta ganin abinda yafaru da mawai Davido hakan yasa Kowa ya Fara rokar masoyansa dasu turamai da kudi domin nuna soyayar su a gareshi.

Mungode da bibiyar shafinmu dakukeyi akoda yaushe. Karku manta ku Danna alamar kararrawar dakuke gani domin Samun labaranmu cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button