Innalillahi jarumin Sani Garba Sk Yana Cikin Mummunan Halin Rashin Lafiya

A jiyane wata uwar marayu Fauziya D Sulaiman ta wallafa wani gajeran bidiyo Jarumi kannywood Sani Garba Sk a shafinta na Instagram inda akaga jarumin Yana bayana tareda rokon Yan uwa da abokan arziki su taimaka Masa akan halin rashin lafiyar dayake ciki.

Saidai a watannin baya anga bidiyon jarumin ya fito Yana rokon alumar musulmai dasu taimaka Masa domin yasamu kudin zuwa asibit Dana magana inda har wasu sukaita zagin jaruman kannywood da masana’antar akan cewar sun gagara taimakawa Dan uwansu.

Saidai a zahirin gaskiya cutar datake Damun sani sk cutace Wanda takeda cin kudi domin ciwon hanta da ciwon sugar ne suke Damun jarumin inda a watannin baya jaruman kannywood sun taimaka Masa.

Saidai a yanzu ma jarumin yasake fitowa Yana Neman taimako kamar yadda alumar musulmai Suka Saba taimaka Masa a inda akwai wasu daga cikin manyan jaruman kannywood dasuka taimaka Masa da kudi kamar Haka

1.Producer Abdul Amart maikwashewa yabawa sani Garba Sk tallafin naira dubu dari biyar N500,000

  1. Jaruma Hadiza Gabon tabada tallafin naira dubu dari biyu da hamsin N250,000
  2. sarki Ali Nuhu yabada tallafin kudi naira dubu dari N100,000
  3. Aisha Tsamiya tabada tallafin kudi naira dubu dari N100,000

Wannan sune sunayen da uwar marayu Fauziya D Sulaiman ta wallafa Wanda suka taimakawa Sani Garba Sk daga cikin masana’antar kannywood akwai Kuma Wanda suka taimakamai da ba’a ambaci sunansu ba.

Ga Wanda basuda halin taimaka jarumin zasu iya yimai addu’a daga duk inda suke domin Allah yabashi lafiya shida sauran Musulman duniya baki daya.

Karku manta ku Danna alamar kararrawar dakuke gani domin Samun shirye shiryenmu cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button