Kalli bidiyon Almajiran da Hadiza Gabon tabiyawa kudi dubu dari (100,000) domin kallon FANAN

Jaruma Hadiza Gabon tayi wani abun daba’a taba Honda a masana’antar kannywood ba domin kuwa tacikawa wasu Almajirai burinsu.

Fitacciyar jarumar kannywood Hadiza Gabon ta biyawa wasu Almajirai kudi har naira dubu dari domin su samu damar kallon Shirin FANAN tareda sauran jaruman kannywood.


Mansurah isah ce ta wallafa hakan a shafinta na Instagram ta bayyana cewar Hadiza Gabon ta turo Mata da kudi naira dubu dari domin biyawa Almajirai su samu damar kallon Shirin FANAN da ake nunawa tareda sauran jaruman kannywood kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon.

Ga video

Acikin kudin Mansurah isah ta bayyana cewar zasuyi amfani da naira dubu saba’in aciki domin biyan kudin tickets, inda naira dubu talatin Kuma za’ayi amfani dashi wajan Saya musu drinks Dakuma abincin.

Jarumar kannywood Hadiza Gabon tasaba da irin wannan taimakawa marayu da Almajirai ta hanya daban daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button