Mansurah isah da sani Danja sun kafa tarihin da ba’a taba kafashi ba a masana’antar kannywood

Wani abun Farin ciki daya faru Wanda zamuce anyi fina finai daban daban acikin masana’antar kannywood a shekarun dasuka wuce Wanda zamuce sunyi suna Duniya ta sansu.

Saidai Shirin film din “FANAN” yazama shiri na farko Wanda ya hada kudi naira miliyan Tara da dubu dari biyu da arba’in da biyar 9,245,000 Wanda ya kasance shine film na farko a cinema daya taba hada irin wannan kudin.

Shirin film din FANAN Shirine Wanda yasamu kwararrun ma’aikata tareda Kayan aiyuka masu kyau, Mansurah isah itace ta Shirya wannan Shirin a inda darakta sheik isah Alolo yabada umarnin wannan Shirin.

A Yanxu Haka anaci gaba da nuna wannan Shirin a platinum cinema Dake cikin garin Kano tundaga misalin karfe goma Sha daya na safe 11am zuwa karfe goma na dare 10pm a kullum.

Tabbas yakamata a jinjinawa Mansurah isah da irin namijin kokarin datayi wajan kawo wannan Shirin tareda Kuma Umar m shariff domin wakar Shirin “FANAN” itace silar tallata Shirin lungu da sako a fadin najeriya Dama wajanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button