Ali Nuhu, Hadiza Gabon, Abdulamart Da Aisha Tsamiya Sun Dauki Nauyin kudin asibitin jarumi Sani Garba Sk

Innalillahi biyo bayan Neman taimako da jarumin masana’antar kannywood yakeyi Sani Garba Sk Kan ciwon dayake damunsa na tsawon lokaci.

Wasu daga cikin jiga jigan kannywood sun tallafawa jarumin da Kudade domin asamu akaishi asibiti inda acikin Wanda aka ambato sun hada da Jarumi Ali Nuhu,Hadiza Gabon,Aisha Tsamiya da Abdulamart.

Saidai jaruman kannywood sunaci gaba da shan zagi a kafofin sada zumunta biyo Bayan bidiyon da Mara lafiya Sani Garba Sk ya Fitar nacewar Yana neman taimako awajan alumar Annabi.

Anyita zagi da cin mutunci ga wasu daga cikin jaruman kannywood Kan kin taimakawa Dan uwan nasu sani Garba Sk, inda mutane suke bayyana cewar kannywood industry Basu kyauta ba Akan abinda sukayi.

Saidai abinda mutane Basu sani ba kamar yadda Fauziyya D Sulaiman uwar marayu tayi bayani akai shine cutar sani Garba Sk cutace Wanda take matukar cin kudi sosai domin ciwon hanta da ciwon sugar ne suke damun jarumin.

Takara bayyana a can bayama dayawa daga cikin jaruman kannywood sun fito sun taimaka Masa, Dan Haka baikamata mutanen gari sudinga zagin jaruman kannywood ba akan cewar basa taimakawa yan uwansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button