Khadija Yobe (Kareema izzar so) tana Neman taimakon alumar musulmai innalillahi

Halin da wasu daga cikin jaruman kannywood Suka tsinci kansu kenan tun bayana abinda ya faru da mawakin kudancin najeriya Davido inda yasamu makudan Kudade daga wajan abokansa.

Biyo Bayan ayyana cewar zai gudanar da shagalin murnar zagayowar ranar haihuwarsa (birthday) inda mawaki Davido yace yanason abokansa su hadamai naira miliyan daya a matsayin gudunmawar su inda acikin awanni ashirin da hudu mawakin yasamu kimanin naira miliyan dari da tamanin.

Wannan yasa wasu daga cikin jaruman kannywood Suma Sukabi sahun abinda mawaki Davido yayi inda jarumar kannywood Khadija Yobe Wanda kukafi sani da (Kareema izzar so) itama ta wallafa cewar masoyanta su taimaka su tura Mata da kudi.

Saidai tun Bayan wallafa wannan rubutun wasu daga cikin mabiya jarumar a shafukan Nata nasada zumunta wato Instagram sukaita suka tareda cin mutuncin jarumar.

Inda mabiya jarumar suke bayyana cewar wannan rashin godiyar Allah ne domin akwai mutane mabukata Wanda suke cikin halin damuwa da Rashin lafiya suya kamata ataimakawa Bawai jarumar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button