Mawaki Davido Yabada kyautar Naira Miliyan 250,000,000, abawa gidan marayu

Fitaccen mawakin kudancin najeriya Kuma mawakin Duniya Davido ya matukar bawa mutane mamaki inda yayi kyautar Naira miliyan dari biyu da hamsin da yammacin ranar Asabar 20/11/2021.

Kwana uku dasuka wuce mawakin ya bayyana cewar zaiyi bikin ranar munar zagayowar haihuwarsa wato (birthday) Dan Haka Yana bukatar masoyansa, abokanansa da Wanda Yasan sunajin wakokinsa dasu hadamai kudi naira miliyan daya domin gudanar da shagalin.

Bayan Bayarda wannan sanarwar ne dai cikin mintuna goma jarumin yasamu kimanin naira miliyan bakwai inda Haka masoyan nasa sukaci gaba da turamai Kudade tsawon kwana biyu inda jumullar kudin suka kai kimanin naira miliyan dari biyu.

Mawakin ya girgiza Duniya a inda yau yafito ya bada sanarwar cewar yasamu kudi kimanin naira miliyan dari biyu N200,000,000 Dan Haka shima acikin kudinsa ya bada naira miliyan hamsin N50,000,000 inda aka hada kudin yakai naira miliyan dari biyu da hamsin 250,000,000 kyauta domin a tallafawa marayun dasuke fadin najeriya.

Mawakin ya Fitar da sanarwar da yammacin yau Asabar 20/11/2021 wannan sanarwar tabawa mutane mamaki domin kuwa Babu Wanda ya taba tunanin mawakin zaiyi kyautar wannan makudan kudaden.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button