Innalillahi Gaskiyar labarin mutuwar jarumin kannywood sani Garba Sk

Innalillahi a safiyar yaune dai wani labari yake yawo a kafofin sada zumunta akan mutuwar sani Garba Sk Jarumi acikin masana’antar kannywood.

Biyo bayan wani bidiyon da jarumin yasake acikin wannan Makon inda yake neman taimakon alumma Kan rashin lafiyar data damunsa, a yau Kuma wasu sukaita wallafa labarin karya akan jarumin.

A halin yanzu sani Garba Sk yananan Bai mutu ba domin kuwa Yana asibiti indai zakuji cikakken Hira daga Bakin jarumin Dakuma irin taimakon daya samu.

Ga video

A Makon daya wucene mutane sukaita zagin jaruman masana’antar kannywood inda suke bayyana cewar basuyi adalci ba na rashin taimakawa Dan uwan sana’arsu sani Garba Sk.

Saidai labarin Gaskiya shine Mara lafiyan ya bayyana cewar tun farkon Fara rashin lafiyarsa kannywood suke daukar nauyinsa har izuwa yanzu Dan Haka Babu abinda zaice da kannywood saidai Allah ya saka musu da alkairi.

A wannan Makon ma wasu dagacikin fitattun kannywood sun tallafawa sani Garba Sk da kudi inda Ali Nuhu ya bada naira dubu dari N100,000 Hadiza Gabon tabada dubu dari biyu da hamsin N250,000 Aisha Tsamiya tabada naira dubu dari N100,000 producer Abdulamart yabada naira dubu dari biyar N500,000 Allah ya saka musu da alkairi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button