Jaruman kannywood sun jajantawa Adam a zango da Ado Gwanja Kan hatsarin dasukayi a hanyar nijar

Biyo Bayan mummunan lamarin daya faru da manyan jaruman kannywood Adam a zango da Ado Gwanja akan hanyarsu tazuwa kasar nijar domin halartar wani taron biki.

Adam a zango da Ado Gwanja sun gamu da mummunan hatsarin motan Wanda tayi sanadiyyar bige wata Mata tareda ya’yanta guda uku Wanda Nan take Allah ya dauki ransu.

Lamarin ya matukar tayarwa da mutanen nijar Dakuma abokan sana’ar jaruman guda biyo. Inda mutane suka shiga alhinin faruwar wannan lamarin.

Manyan jarumai maza da Mata daga masana’antar kannywood sun jajantawa Ado Gwanja da Adam a zango tareda Mika ta’aziyyar su ga mutanen nijar Kan faruwar wannan lamarin.

Inda sukai addu’ar Allah ubangiji ya Kara kiyaye nagaba, Allah Kuma yabawa iyalan wannan Matar da hatsarin ya faru da ita hakurin rashinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button