Lawan Ahmad Ya zagi Mahaifiyar Sadiq Sani Sadiq Akan rokon kudin dayayi awajan masoyansa

Tirkashi wani babban alamari daya faru acikin masana’antar kannywood Wanda ba’a Saba ganinsa ba inda Jarumi lawan Ahmad ya zagi Mahaifiyar Sadiq Sani Sadiq a shafin sada zumunta.

Hakan ya biyo bayane bayan da jarumin kannywood lawan Ahmad yafito ya nemi da masoyansa su taimaka Masa su tura Masa da kudi kamar yadda akayima mawaki Davido.

Biyo bayan irin kudaden da mawaki Davido ya samu inda jumullarsu takai kimanin naira miliyan dari biyu hakan ya tashi hankalin wasu daga cikin jaruman kannywood inda shima lawan Ahmad Jarumi acikin izzar so ya nemi da ataimaka Masa.

Saidai tun Bayan bayyanar cewar lawan Ahmad yanaso a taimaka Masa shima yaci albarkacin Annabi masoyansa suturamai da kudi. Saidai abinda lawan Ahmad yayi yasa wasu daga cikin masoyansa sun Fara fadin maganganu marasa Dadi akansa.

Saidai Jarumi Sadiq Sani Sadiq ya Fitar dawani video inda akaga jarumin Yana Dariya Yana murmushi saidai Kuma baikama sunan Kowa acikin bidiyon nasa ba saidai Kuma duk Wanda ya kalli bidiyon Yasan cewar yanayi ne da jaruman kannywood dasuka fito Suka nemi a taimaka musu da kudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button