Wata sabuwa! Ana zargin Lawan Ahmad da cinye kudin Gasar Al-Qur’ani da aka saka

Da yammacin yau lahadi ashirin da daya ga watan nuwambar shekarar dubu biyu da ashirin da daya Muka samu wani rahoto daga tashar Hausa joint Dake manhajar YouTube cewar Ana zargin lawan Ahmad da cinye kyautar daza abama Wanda sukaci gasar kararun Al-Qur’ani maigirma.

Idan baku mantaba a watannin baya dasuka wuce Jarumi lawan Ahmad shida darakta Nura mustapha waye sun saka gasar kararun Al-Qur’ani maigirma ga duk Mai ra’ayin yin gasar zai iya shiga Kai Tsaye.

A inda a lokacin lawan Ahmad ya Fitar da sharudan gasar inda wannan gasar zaka iya yinta daga ko Ina kake domin ana bukatar bidiyon mutum ne kadai, Wanda zasu fafata a gasar ana bukatar su karanta ayoyi biyu daga cikin Al-Qur’ani.

Sannan zakayima kanka bidiyo kana wannan kararun Al-Qur’ani tareda daurawa a shafinka na Instagram sannan ka rubuta wannan alamar a kasan bidiyon #lawanahmad kokuma #nuramustaphawaye wannan shine zaibawa lawan Ahmad da Nura mustapha waye damar ganin bidiyon mutane a shafin na Instagram.

Lokacin da aka saka wannan gasar mutane da dama sunji Dadi tareda nuna Farin cikinsu Kan Irin samun cigaba da akayi a kannywood wajan saka gasar kararun Al-Qur’ani maigirma.

Saidai tun bayan kammala wannan gasar haryanzu ba’a Fitar da Wanda sukai nasara acikin wannan gasar Haka zalika ba’a nunawa duniya kyautar da aka bawa Wanda sukaci gasar ba.

Hakan yasa aka taso da wannan batun a shafukan sada zumunta inda ake kalubalantar Jarumi lawan Ahmad daya fito ya bayyana abinda ya faru dangane da gasar kararun Al-Qur’ani dasuka saka domin gamsar da mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button