A Karon farko jaruma Rahama Sadau tafito acikin Shirin Indian film maisuna khuda Haafiz

Kamar yadda jarumar ta wallafa wasu hotunanta har guda bakwai a shafinta na Instagram tareda wani jarumin India tare da rubuta “Hello Bollywood”

Idan baku manta ba a shekarar data gabata dai jarumar kannywood Rahama Sadau aka koreta daga kannywood sakamakon wani shiga datayi Wanda har hakan ya fidda tsaraicin ta har wani makiyin addinin musulunci yayi batanci ga Annabi Muhammad a Dalilin hotonta.

Bayan Jan hankali da kiraye kiraye da abokan sana’ar jarumar sukai Mata akan tacire wannan hoton a shafinta na sada zumunta domin Samun saukin barakar data barke.

Jarumar Bata cire hoton da wuri ba har Saida abokan sana’arta Dakuma masoyanta suka fito sukai Mata zazzafan martani akan irin abinda ta aikata sannan jarumar ta goge hoton a shafinta na Instagram.

Bayan zama da kungiyar kannywood tayi tareda duba abubuwan da jarumar ta aikata yasa Suka koreta daga masana’antar kannywood gaba daya.

Wannan Dalilin Yasa jaruma Rahama Sadau Takoma fitowa acikin Fina finan kudancin najeriya wato “Nigerian film” saidai bayyanar hotunan jaruma Rahama Sadau a kasar India inda ake daukar wani sabon Shirin India maisuna “Khuda Haafiz”

Abokan sana’ar jaruma Rahama Sadau tareda masoyanta sun tayata murna da Farin cikin samun wannan babban damar datayi a rayuwarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button