Nafi karfin a yaudareni da computer dubu dari da hamsin N150,000 wallahi kuwa inji Ayatullahi tage

Jarumin barkwanci acikin masana’antar kannywood Ayatullahi tage yace yafi karfin a yaudaresa computer duba dari da hamsin domin Shi Allah ya rufamai Asiri yanada wadatar zuci.

Biyo bayan wani taro da aka gudanar jiya lahadi Wanda Sanata barau I jibril ya tallafawa masana’antar kannywood da akan irin halin da tashiga Jarumi Ayatullahi tage yafito ya nuna cewar Shi wannan taron ya hakura dashi.

Ayatullahi tage ya Kara bayyana cewar abinda akace za’a bashi awajan taron domin tallafamai Shi Allah ya taimakesa yanadashi, Dan Haka abawa masu bukata kamar yadda zakuji daga bakinsa.

Ga video

Ayatullahi tage ya Kara dacewar Shi baya zuwa duk wani taron tallafawa kannywood, duk ranar Dakuma aka gansa awajan taron to akamashi.

Saidai kalaman da Ayatullahi tage yayi amfani dasu wasu daga cikin Masoyansa sun nuna rashin Jin dadinsu tareda bayyana baikamata ace yafito Yana wannan maganar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button