Auren Umar Hashim Da Hajiya Nafisa Izzar so Ya Matukar girgiza kannywood

Dukwani makallacin shirin wasan Hausa Yasan shiri Mai dogon zango “izzar so” shirine Wanda yazo da Abubuwan daba’a taba ganin irinsu na acikin labaran Fina finan hausa.

Shirin izzar so wani shirine Wanda aka ginasa akan gaskiya da rikon Amana dakuma, yadda wasu mutane suke amfani da damar da Allah ya Basu wajan murzgunawa da cin mutuncin nakasa dasu.

Duk maikallan Shirin izzar so Yasan irin wutar gaban dake tsakanin hajiya Nafisa Dakuma Umar Hashim acikin Shirin inda wannan gabar tasamo asaline tun farkon Shirin izzar so season 1.

Inda farkon zuwan Umar Hashim wannan ma’aikata a lokacin hajiya nafisa tana shugaban karamar ma’aikata shigowanta Kowa ya tashi ya gaisheta amman Umar Hashim baitashi ya gaisheta ba kamar yadda sauran ma’aikatan sukayi wannan shine silar gabar Dake tsakanin Umar Hashim da hajiya nafisa.

Inda wannan gabar gashi tacigaba da ruruwa, duk da irin kalubalen da Umar Hashim ya fuskanta awajan hajiya nafisa saidai duk wasu abubuwa Mara kyau datake shiryamai cikin hukuncin ubangiji basa faruwa Akansa.

Anan Kuma Wani hoton Umar Hashim ne tareda hajiya nafisa inda aka wallafa wani gajeran bidiyo su a shafin Instagram Wanda alamu suka nuna kamar shagalin Auren jaruman akeyi kamar yadda zaku gani.

Ga video

Saidai abun ba Haka bane domin kuwa, wasu mutane suna wallafa cewar Umar Hashim ya auri hajiya nafisa zancen ba gaskiya bane.

Wannan gajeran bidiyo da akaga Umar Hashim da hajiya nafisa an daukesana lokacin da suke tallan wani katafaren wajan shagalin biki, taron siyasa, taron walima dadai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button