Auren jaruma Meerah Da Magaji Mijin yawa ya girgiza kannywood – Gidan Badamasi season 4

Duk Wani Mai kallon Shirin gidan badamasi Shirin barkwanci Mai dogon zango Wanda ake nunasa a tashar arewa24 duk Ranar alhamis da misalin karfe takwas na dare Yasan Soyayyar Dake tsakanin Junaidiya da Alhaji Badamasi.

Bayan tafiya dogon hutu Mai tsayi da Shirin yayi tun bayan karewar zango na uku wato season 3 ba’a samu damar cigaba da daukan zango na hudu akan lokaci ba sakamakon wasu dalilai.

Saidai cikin hukuncin ubangiji yanzu Haka anfara daukan Shirin gidan badamasi zango na hudu a inda daraktan Shirin Falalu a dorayi shine yayi wannan sanarwar Haka zalika hotunan da aka wallafa na Junaidiya da Alhaji Badamasi daraktan Shirin shine ya daurasu domin ya tabbatarwa da makallata Shirin cewar zango na hudu yananan tafe.

Abubuwan da makallata Shirin gidan badamasi suke jiran faruwarsu shine kamar yadda za’a daura auren Alhaji Badamasi da Junaidiya saikuma bayyanar zuwa gidan yarin da yaran Alhaji sukayi gaba dayansu inda zuwansu gidan yarin sun sake haduwa da Jarumi Adam a zango Wanda shima yakasance Yana daya daga cikin yaran Alhaji Badamasi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button