Innalillahi An Maka Jarumar kannywood Hafsat Idris (Barauniya) Gaban Kotu Kan Cinye Wasu Kudade datayi

Wani rahoto Mara Dadi dangane da daya daga cikin fitattun jaruman kannywood Mata wato hafsat Idris inda Kamfanin UK Entertainment Suka kaita Kara gaban kotu Kan cinyemusu kudi Kuma batayi aikin dasuka bata ba.

Wani rahoto da gidan Radio Dala FM dake Kano ya kawo ya bayyana cewa wani kamfani ya kai ƙarar jarumar Kannywood Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya, zuwa gaban babbar kotun jihar Kano, wacce ke Ungoggo, kan zargin cinye zunzurutun kuɗi har naira miliyan daya da dubu dari uku da aka bata domin daukar bidiyon rawa, amma ta saɓa alkawari.

Rahoton ya bayyana cewa jarumar ta zo gurin bikin, har an fara daukar bidiyon, sai kuma ta gudu ba ta dawo ba, inda hakan yasa kamfanin ke buƙatar kotu ta sa ta dawo musu da kuɗin su, kana ta biya su naira miliyan goma.

Sun bukaci wannan naira miliyan goma ne a matsayin diiyyar asarar da ta sa suka yi domin sun tara ma’aikata sun ɗauko hayar kayan aiki, sai kuma rashin cika alƙawarinta yasa sun yi asara.

Har ya zuwa yanzu dai bamu ji ta bakin ita jaruma Hafsat Idris kan wannan batu ba. Saidai masoyan jaruman sunshiga rudani ganin irin wannan tuhumar da akeyi Mata.

Inda wasu suke ganin kamar ba gaskiya bane wasu Kuma suna fadin cewar gidan freedom radio bazasuyi jarumar karya ba Dan Haka wannan labarin gaskiya ne.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button