Innalillahi Wallahi bani bace Nace Sani Garba Sk ya mutu cewar Zainab Sambisa

Biyo Bayan labarin mutuwar jarumin kannywood sani Garba Sk Wanda ya zagaye kafofin sada zumunta a yammacin ranar litinin ashirin da daya ga watan nuwambar shekarar dubu biyu da ashirin da daya inda aka wallafa cewar Allah yayiwa jarumin rasuwa Bayan Dana da Rashin Lafiya dayayi.

Labarin mutuwar yafara fitowa ne daga wani shafi a Facebook maisuna “zainab Sambisa” inda anan aka Fara wallafa labarin mutuwar sani Garba Sk saidai bayan tabbatar da wannan labarin karyane mutane sunyita zagin zainab Sambisa tareda fadin maganganu marasa Dadi akanta.

Saidai jarumar tafito tayi magana a inda ta bayyana cewar ba ita bace ta wallafa labarin mutuwar sani Garba Sk domin ita Bata Facebook batama taba Bude Facebook ba.

Jarumar ta bayyana cewar wanine ya Bude Facebook da sunanta yake amfani dashi wajan yada labaran karya Amman Ni bana Facebook Kuma ban tana bude Facebook ba Dan Haka mutane su kula ba zainab Sambisa bace take amfani da wannan account din.

Biyo bayan wallafa labarin karya akan cewar jarumin ya mutu ansamu wani bidiyo da akaga jarumin Yana bayanin cewar yananan a raye baimutu ba kamar yadda ake yada labarin inda Akansa zaune akan Gadon asibiti. Allah ubangiji ya basa lafiya Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button